Amfanin Asuwaki da Fa'idojin sa



Aswaki abune na goge baki wanda ake yinsa daga jikin bishiya aswaki yana da tsohon tarihi tun daga kan Annabawa har zuwa zamanin da muke ci yana da amfani mai yawa ga jikin dan adam.

Abu Huraira ya kawo hadisi cewa Manzon Allah s.a.w yace “da badun kar in tsanantawa Al'ummata ba dana umarce su da yin aswaki kafin kowane alwala”Bukari da Muslim suka rawaito
Abu Ayuba yace Manzon Allah s.a.w yace“ abubuwa guda hudu na daga cikin sunnar Aannabawa kaciya sanya turare da yin aswaki” Ahmad da Tirmizi suka rawaito Ibn Abbas yace Manzon Allah s.a.w yace “an umarce ni da in yin aswaki sanda na yi tunanin za a saukar da aya akanta ” Abu ya'ala ya ruwaito. Akwai hadisai da dama da suka yi magana akan aswaki da falalar dake cikinta sai yasa zaka samu manyan sahabbai da sauran maluma suna kwadaitarwa akan amfani da aswaki ibn Isma'il yana cewa “abin na ban mamaki yadda mutane suka bar sunna mai muhimmanci na yin aswaki” hadisan Annabi dayawa sun yi bayani akai akwai hasara da yawa ga barin aswaki” imam Shaukani ya fada a cikin nailul awdar “aswaki na daga cikin sharia na safe da yamma haka mutanen duniya suke gani”Abu Dawud shi kuwa cewa ya yi “abubuwa biyu na daga cikin abu mai kyau yin tahajjud da aswaki” saboda muhimmancin aswaki nema yasa Imam gazali a cikin littafinsa ihya'u ulumuddin da ya tashi lissafo ladubban bacci guda goma sai yasa aswaki a farko. Duk da muhimmancin dake tattre da aswaki amma akwai nau'uka na bishiya da ba a so ayi amafni da shi wajen yin aswaki saboda cuta da suke sawa a jiki nau'ukan bishiyar sun hada da bishiya mai kamshi domin tana sa ciwon kuturta itacen ruman.

LOKUTAN YIN ASWAKI
~Lokacin yin alwala
~Lokacin fara salla
~Lokacin tashi daga bacci
~Idan mutum ya farka bacci
~Lokacin fara karatun alkur'ani
~Lokacin shiga gida ko wani masauki
~Lokacin karanta hadisin Manzon rahama
~Lokacin da za a yi wani aiki na alkairi

YADDA AKE YIN ASWAKI

~Ana bin tsawon hakura
~Karamin yatsa da babban yatsa ana sanya su a kasan aswaki ne sauran yatsun kuma ana mai da su saman aswakin
~Ana yin sa fadin baki ne
~Ba a yi cikin salla
~Ba a yi cikin karatun Alkur'an

BINCIKEN MASANA GAME DA ASWAKI
Masana sun yi bincike sun gano cewa aswaki yafi amfani fiye da yin amfani da brush da makilin kungiyar kare lafiya ta duniya {w.h.o} ta yi bincike a shekarar 1986 ta bukaci a dinga yin amfani da aswaki ashekarar 200 kidayar kiwon lafiya da aka bayar sun nuna amfanin aswaki wajen kiwon lafiyaDr Rami Mohammed Diabi wani malami da ya yi shekara goma sha bakwai 17 yana bincike akan amfanin aswaki a jikin dan adam musamman ma ga masu shan sigari wanda ta kai shi ga rubuta littafi mai suna (siwak world of science and research) a cikin littafin ya tabbatr da cewa aswaki na kare duk wata irin cuta dakan iya samun baki da duk abin dake tattare da shi.

AMFANIN ASWAKI GA. JIKIN DAN ADAM

Anan zan kasa shi zuwa gida biyu amfaninsa ga mutum shi kansa ta bangaren addini da kuma amfaninsa wajen kiwon lafiya ga jikin dan adam

AMFANINSA TA BANGAREN ADDINI

~Yana janyo haske a fuskar mai yi
~Ana ninka ma mutum ladansa daga 70 zuwa 400
~Yana kai mutum babban matsayi a aljanna
~Koyi ne da Annabi s.a.w
~Yana bude hanyar arziki
~Mala'iku na gaisuwa ga mai yinsa
~Yana janyo cikawa da imani
~Yana sa gida ya yi albarka
~Yana hana mantuwa da salla
~Yana karawa mutum daukaka a cikin mutane
~Yana sawa mutum dabia mai kyau
~Yana karya makiyi
~Yana sa makiyinka ya tsorata da kai
~Yana sawa makiyin ka faduwar gaba in ya tuna da kai
~Yana sa a samu nasara a abun da ake nema na alkairi
~Yana sa makiyinka ya guje ka

AMFANINSA GA LAFIYAR JIKIN DAN ADAM

~Yana sa kamshin baki
~Yana kariya ga bacin hakora
~Yana tsayar da cutar da ke dadashin mutum
~Yana maganin duk wani cuta
~Yana sa kwarin jiki
~Yana sa fitsari ya fito sosai
~Yana inganta hanji
~Yana kwantar da cuta mai bugarwa
~Yana narkar da abinci
~Yana sanya dandano a baki
~Yana wanke zuciya
~Yana kawar da ciwon kai
~Yana warkar da ciwon hakora
~Yana tsarkakee baki
~Yana gyara hakora
~Yana kawar da majinar makogoro
~Yana kara ganin idanu
~Yana kara basira
~Yana inganta lafiyar jiki
~Yana saukaka cuta mai wuyar magani
~Yana rage bacci
~Yana kara hankali
~Yana kara fasaha
~Yana sa furfura kar ta yi yawa a jikin mutum
~Yana turmuza shaidan
~Yana maganin Sihiri

Yan uwa masu daraja mu rika kokarin yin aiki da wannan sunna mai muhimmanci da falala musamman yan uwa mata don dayawansu basu damu da wannan sunna ba wasu ma gani suke asuwaki ya takaita ga maza ne kawai wasu ko ganinsa suke a matsayin zubda aji Manzon Allah s.a.w yana rashin lafiya mai tsanani amma haka bai hana shi yin aswaki ba kamar yadda Aisha Ummul mumina radiyallahu anha ta fada.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Amfanin Asuwaki da Fa'idojin sa"

Post a Comment