Amfanin Dafa Tafannuwa da Lemun Tsami

.


Idan ka samo kwayar tafarnuwa kamar guda 10  ka bare bawon, kuma ka samo lemon tsami  guda 6 ka tsaftace shi kuma ka yayyanka shi, sai ka zuba tafarnuwar da kuma lemon tsamin har da bawon a cikin ruwan zafi kamar kofi daya ko daya da rabi sai ka barsu a kan wuta har tsawon mintuna 5.

Bayan mintuna biyar din sun cika sai ka sauke shi ka tace shi kuma kabari ya huce, idan ya yi sanyi sai ka rika shan babban cokali 1 da safe kafin kaci komai.

Kadan daga cikin amfanin wannan hadin su ne kamar haka:

1- Yana karawa jiki garkuwa daga kamuwa da cutar Cancer ko wacce iri ce, DA YARDAR ALLAH.

2- Yana kawar da duk wata matsala ko lalurar da take a cikin baki kuma yana kara kyautata sautin muryar mutum ta rika fita fes-fes kuma zaqwai musamman na idan yana karatun Alqur'ani. DA YARDAR ALLAH.

3- Yana magance duk wani nau'i na cutar Allergies dake cikin jikin mutum.

4- yana matukar amfani ga masu fama da cutar (paralyse) barin jiki wanda cutar Stroke karama ko babba ke haifarwa DA YARDAR ALLAH.

5- Yana daidaitawa kuma ya tace sugar din dake cikin jinin mutum, shi yasa ake so masu fama da cutar Diabetics su rika amfani da wannan hadin kai akai.

6- Yana taimakawa wajan fasawa tare da kawar da tsakuwar dake cikin Qoda kuma ya warware wa mutum matsalar dake damunsa a mara da yardar ALLAH.

7- Yana ragewa kuma yadaidaita hauhawar jini a jikin mutum DA YARDAR ALLAH.

8- Yana rage sinadaran cholesterol da kitsen dake jikin mutum DA YARDAR ALLAH.

9- Yana magance cutar Ulcer ta gyambon ciki kuma yana wanke dattin ciki da YARDAR ALLAH.

10- Yana magance matsalar duk wani nau'i na sanyin dake jikin mutum, matukar mutum yana amfani da wannan hadin to zai ga bambanci a jikinsa game da matsalar sanyin Infection.

11- Kuma yana taimakawa mutum wajan rage kiba da tumbi da YARDAR ALLAH.

Idan ma mutum bazai iya shan wannan hadin ba, to zai iya kara masa ruwa kadan da zuma a ciki sai yarika sha akai akai DA YARDAR ALLAH zai ga fa'ida fiye da abinda na lissafa musmaman ma masu fama da cutar Ulcer DA YARDAR ALLAH.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da Rahamar sa. 


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Amfanin Dafa Tafannuwa da Lemun Tsami"

Post a Comment