Hadda Ake Yanke Farce (Kumba) a Sunna



Yaya ake yanke farce asunnah, shin mutum zai  fara da ɗan yatsarsa na dama ne ko hagu?

𝐀𝐌𝐒𝐀

الحمد لله.
Yanke farce sunnah ne daka cikin Sunnonin fidira kamar yanda hadisai ingantattu suka nunar, Anaso farawa dayanke farcen dama saboda hadisin da yatabbata daka A'isha Allah yakara mata yarda tace: Annabi sallallahu Alaihi wasallam yakasance damaitawa tana burgeshi cikin dukkan Al'amuransa wajan ( sanya takalmansa datafiyarsa da dukkan al'amuransa) Bukhari (163).

Nawawi acikin al-majmu'u (1/339) yace: Malamai sunyi ijma'i akan yanke farce sunnah  ne, akan maza da mata na hannuwa dana kafafuwa,  Mustahabbine mutum yafara yanke na hannun dama sannan na hagu, sannan nakafar dama sannan ta hagu.

acikin sharhin muslim (3/149) yasake cewa: Anso mutum yafara da hannun dama, yafara da karamin ɗan yatsarsa sannan mai bi masa har nakarshe.

Sannan saiya koma kafarsa ta dama yafara da karamin ɗan yatsarsa, Sannan Sai kafarsa ta hagu ita kuma zaifara da babban ɗan yatsarsa yakare dakaramin ɗan yatsansa.

Hanabila sukuma sun ambaci wani tsarin nadaban wajan ɗan yatsan daza'a fara yankewa dawanda za'a kare dashi yayin yanke farce, saidai cewa bai tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ba.

Al'iraqi rahimahullah acikin *Darhul tasreeb* ( 2/77) yace: Babu wani hadisi daya tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam wajan yanda za'a yanke farce daza'ai aiki dashi.

Ibnu hajar rahimahullahu acikin fat-hul bari ( 10/345) Yace: Babu  Wani hadisi daya tabbata daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam wajan tsarin yanda za'a yanke farcen wani ɗan yatsan akan wani, Sannan yace ibnu daqeqil Eiid yayi inkarin yanda ake yanke farce wanda imamu gazali ya ambata da waɗanda suke tare dashi, dukkansu basu da asali, farar da mustahabbanci bashi da dalili, abune munnuna awajena asanina, koda mai riyawa zai riya cewa farawa da yatsar dama saboda darajarta, sauran kuma bazai riya musu hakan ba.

Hakane farawa da hannun dama da yatsar dama yanada asali, saboda damaitawa tana burge Annabi Sallallahu Alaihi wasallam.

Saboda haka dai maganar imamu nawawi rahimahullahu tana da asali wajan yanda za'a yanke farce domin yagina fatawarsa akan hadisi ingantacce wanda damaitawa yana daka cikin Sunnah.

Saboda haka yankan farce zaka fara da hannun dama da karamin ɗan yatsa, sannan hagu da babban ɗan yatsa ka kare da karamin ɗan yatsarka, hakama kafafuwa.
 

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hadda Ake Yanke Farce (Kumba) a Sunna"

Post a Comment