Shin Ya Halatta Innemi Maganin Farin Jini


Assalamu alaikum, shin ya halata mace ta nemi maganin farin jini don samun mijin aure?

๐€๐Œ๐’๐€

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

A'a wannan baya daga abinda musulunci yakoyar. idan kuka biyewa irin waษ—annan abubuwan zaku shiga bin bokaye da makamantansu.

Saboda haka idan har mace tanason aure to tagyara halayyarta kuma taji tsoron Allah, tayi addu'a  In shรฃ Allahu zata samu mijin aure.

Sannan yawancin abinda yake kawo rashin samun miji akwai sawa kai buri ko kuma raina wanda Allah yakawo wajanki idan mace zatayi aure karta sake tace sai mai kuษ—i zata aura abinda zata fahimta aure ibada ne arziki da taulaci duk daga ubangiji suke dan haka idan mace zatayi aure tasamu ma'abucin addini wannan ne zaisa taji daษ—in zaman aure arayuwarta.

Sannan rashin aure da wuri bawai bakin jini bane haka Allah yake tsarawa kowa rayuwarsa wata tayi aure da wuri wata kuma tadade batayi ba Amman ubangiji shine masani akan yadda yatsarawa kowa rayuwarsa dan haka kiyi hakuri kiyi addu'a kuma muma muna tayaki addu'a Allah yakawo miki mijin aure nagari dake da sauran matan musulmi baki ษ—aya masu aure kuma Allah yabasu zaman lafia amin.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Shin Ya Halatta Innemi Maganin Farin Jini"

Post a Comment