Hukuncin Kabliyya Bayan Sallama


As-Salaam Alaikum. Idan Sujudul Qabliyyah ta samu mutum, kuma ya manta bai yi ba har sai da ya yi sallama, yaya zai yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah:

Asali dai idan mutum ya yi ƙari a cikin sallah Sujada Ba’adiyyah yake yi. Idan kuma ragi ne ya yi, ko ragi da ƙari a haɗe sai ya yi Sujada Qabaliyyah.

Sannan idan mutum ya manta da Sujadar Ba’adiyyah malamai sun yarda cewa, lallai ya yi ta a duk lokacin da ya tuna. Haka ma Qabaliyyah da ya manta bai yi ba sai a bayan sallama ya tuna, malamai sun yarda ya yi ta a bayan sallamar, ta zama Ba’adiyyah kenan.

Ko ba komai dai, akwai malaman da suka yarda da halaccin yin kowanne daga cikin Sujadar ko Qabaliyyah ko Ba’adiyyahi a kan kowace irin Rafkanuwa:

Al-Haafiz Ibn Hajr ya ce:
وَرَجَّحَ الْبَيْهَقِيُّ طَرِيقَةَ التَّخْيِيرِ فِي سُجُودِ السَّهْوِ قَبْلَ السَّلَامِ أَوْ بَعْدَهُ وَنَقَلَ الْمَاوَرْدِيُّ وَغَيْرُهُ الْإِجْمَاعَ عَلَى الْجَوَازِ وَإِنَّمَا الْخِلَافُ فِي الْأَفْضَلِ وَكَذَا أَطْلَقَ النَّوَوِيُّ.

Al-Baihaqiy ya rinjayar da hanyar zaɓi a cikin Sujudar Rafkanuwa kafin sallama ko a bayan sallama. Kuma Al-Maawardiy da waninsa daga cikin malamai sun ciro ijma’in malamai a kan halaccin hakan. Sun yi saɓani ne kawai a kan wanda ya fi. Haka kuma shi ma An-Nawawiy ya faɗi maganar a sake. (Fat-hul Baariy: 3/94).

Shi kuma An-Nawawiy ya ce:
قَالَ الْقَاضِي عِيَاضٌ رَحِمَهُ اللَّهُ تَعَالَى وَجَمَاعَةٌ مِنْ أَصْحَابِنَا: وَلَا خِلَافَ بَيْنَ هَؤُلَاءِ الْمُخْتَلِفِينَ وَغَيْرِهِمْ مِنَ الْعُلَمَاءِ أَنَّهُ لَوْ سَجَدَ قَبْلَ السَّلَامِ أَوْ بَعْدَهُ لِلزِّيَادَةِ أَوِ النَّقْصِ أَنَّهُ يُجْزِئُهُ وَلَا تَفْسُدُ صَلَاتُهُ وَإِنَّمَا اخْتِلَافُهُمْ فِي الْأَفْضَلِ، وَاللَّهُ أَعْلَمُ .

Al-Qaadiy Iyaadh (Rahimahul Laah) da waɗansu daga cikin malaman mazhabarmu sun ce: Babu saɓani a tsakanin waɗannan malaman da suka saɓa wa juna da waɗansunsu cewa, ya wadaci mutum idan ya yi sujada kafin ko a bayan sallama domin ƙari ko ragi, kuma sallarsa ba ta ɓaci ba. Saɓaninsu dai kawai a kan wanda ya fi ne. (Sharhun Nawawiy: 5/56-57).

WALLAHU A'ALAM

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hukuncin Kabliyya Bayan Sallama"

Post a Comment