Hukuncin Mai Sallar Magriba Yabi Mai Sallar Isha'i


Mutum ne yazo masallaci ana sallar isha'i shi kuma baiyi magariba ba, liman yayi raka'a uku sai yayi tahiya yayi sallama, yakabbara ya miqe yasauran isha'i ɗin meye matsayin sallarsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀

الحمد لله وحده لا شريك له.
Sallarka tayi, daman kodai kayi tahiya kajira liman kuyi sallama tare ko kuma ka sallame araka'a ta uku, sannan saikai sallar isha'i ɗinka.

Wannan itace mazhabar imamu shafi'i rahimahulla, kuma itace ɗaya daka cikin maganganun Imamu Ahmad, Mardawi Acikin Inshaaf ( 4/413) Yace: Wasu daka cikin daliban imamu Ahmad Sun zabeta, daka cikinsu Akwai shaikul islam ibnu taimiyyah da kakansa Majid bin taimiyyah.

Imamun Nawawi rahimahulla acikin Majmu'u fatawa (4/143) Yace: Da mutum Zai niyyaci Sallar asuba abayan wanda yake azahar mamu ya cika sallarsa ta Asuba, idan yaga dama zai jira liman azaman tahiyarsa suyi sallama tare wannan shine yafi, idan yaga dama zai kyale liman yayi sallamarsa, Anan Sallarsa bata ɓaci saboda yariga liman Sallama ba babu Saɓani, saboda Uzurin mutaba'a, haka cikin Sauran salloli waɗanda sukai kama da haka. Kamar yanda malaman lajnatul da'imah suka bayyana ( 7/407).

Saɓanin niyyar mamu data liman bata cutar dashi, a ingantacciyar magana cikin magan-ganun Malamai.

Dan haka wanda yayi haka tareda liman yayi dai-dai Sallarsa tayi babu wani abu akansa.

WALLAHU A'ALAM

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hukuncin Mai Sallar Magriba Yabi Mai Sallar Isha'i"

Post a Comment