Wasu Daga Cikin Lokutan da Ake Karanta Ayatul Kursiyyu


1- A Kowace Safiya Da Yammaci, Wato Bayan Sallar Assuba Da Bayan Sallar La'asar Ko Bayan Magariba.

FALALAR KARANTA TA A WANNAN LOKACIN:

Manzon Allah Saw Yana Cewa:
(Wanda Ya Karanta AYATUL KURSIYYU Da Yamma, Za'a Bashi Kariya Ta Musamman Har Zuwa Safiya, Idan Ka Karanta Da Safe, Za'a Bashi Kariya Ta Musamman Har Zuwa Yammaci)
@رواه النسائي في الكبرى والطبراني وصححه الألباني في صحيح الترغيب والترهيب برقم (662)]

2-Bayan Kowacce Sallah Ta Farillah, Wato Da Zarar An Yi Sallama Kayi Istighfari Sau Uku Sai Ka Karanta AYATUL KURSIYYU.

FALALAR KARANTA BAYAN SALLAR FARILLA:

Manzon Allah SAW Yana Cewa:
(Wanda Ya Karanta AYATUL KURSIYYU Bayan Kowacce Salla Ta Farilla, Babu Abin Da Zai Hana Shi Shiga A Aljannah Sai Mutuwa)

@وهكذا رواه الطبراني في " الكبير" (7532) ، والروياني في " مسنده " (1268) ، وابن السني في " عمل اليوم والليلة " (124) من طريق محمد بن حمير به .
وهذا إسناد جيد.

3- Lokacin Kwanciya Barci, Wato Lokacin Da Zaka Kwanta Barci Kayi Alwala Irin Ta Sallah Sannan Ka Karanta AYATUL KURSIYYU.

FALALAR KARANTA TA LOKACIN KWANCIYA BARCI:

Manzon Allah SAW Yana Cewa:
(Idan Ka Zo Kwanciya Barcin Ka, To Ka Karanta AYATUL KURSIYYU, Har Zuwa Karshen Ta, Ba Zaka Gushe Ba Kana Tare Da Mai Kariya Daga Allah, Kuma Shaidhanu Baza Su Kusanceka Ba Har Sai Ka Wayi Gari)
@أخرجه البخاري

4- Lokacin Addu'ah Kamar Addu'ar Ruqya Da Neman Waraka Ga Marar Lafiya.

Manzon Allah SAW Yana Cewa:
(Sunan Allah Mafi Girma Wanda Idan Aka Roke Shi Da Shi Yake Amsawa, Yana Cikin Surori Guda Uku Na AlQur'ani, Suratul Baqra, da Ali'imran da Ɗâha)
@أخرجه ابن ماجة وصححه الألباني.

Abu Abdurrahman Alƙasim bn Abdurrahman Wanda Ya Ruwato Wannan Hadisin Daga Cikin Tabi'ai, yana cewa: “Mun Bin Cika Sai Muka Gano Sunan Allah Mafi Girma a Cikin Saratul Baqara Yana Cikin AYATUL KURSIYYU.........

@قال الألباني: و هذا إسناد حسن.
Dan Haka Ake Karanta AYATUL KURSIYYU A Lokacin Addu'a Musamman Addu'ar Neman Waraka Da Warware Sihiri Domin Tawassili Da Sunan Allah Mafi Girma.

  Allah Ne Mafi Sani

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Wasu Daga Cikin Lokutan da Ake Karanta Ayatul Kursiyyu"

Post a Comment