Amfanin Daga Hannun Yayin Addu'a


ƊAGA HANNUN LOKACIN ADDU'A SABABI NE NA AMSAR ADDU'AR BAWA

Ɗaga Hannu Yayin da Mutum Zai Roƙi Ubangiji Buƙatunsa Yana Daga Cikin Sabubban Dake Sakawa Ubangiji Ya Amshi Addu'an Bawa a Kowane Wuri. Ubangiji Ya Sanya Ɗaga Hannu Yayin Addu'a Ya Zamo Sila ta Amsa Roƙon Bawa Kamar Yanda Ya Sanya Cin Haram Ya Zamanto Sababin Ƙin Amsar Addu'an Mutum. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:

عَنْ سَلْمَانَ رَضِيَ اللهُ عنه أنه قالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلَّى اللهُ عَليهِ وسلَّم: (إِنَّ رَبَّكُمْ حَيِيٌّ كَرِيمٌ يَسْتَحِي مِنْ عَبْدِهِ إِذَا رَفَعَ يَدَيْهِ إِلَيْهِ أَنْ يَرُدَّهُمَا صِفْرًا)
{رواه أبو داود}

An Karɓo Daga Salman (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: (Lallai Ubangijinku Mai Kunya ne Mai Karamci Yana Jin Kunyar Bawansa Idan Ya Ɗaga Hannunsa (Yana Roƙonsa) Zuwa Gareshi Ya Mayar Dasu Hakanan (Ba Tare da Ya Amsa Masa ba).
{Abu-Daud}

Har Wayau Hadisi Ya Tabbata da Manzon Allah (ﷺ) Ya Ambaci Wani Mutum Wanda Cin Haramun da Yakeyi ya Haramta Masa Amsar Addu'ansa Daga Allah Maɗaukaki. Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:

(..........ثم ذكر الرجل يطيل السفر أشعث أغبر يمد يديه إلى السماء: يا رب يا رب، ومطعمه حرام ومشربه حرام وملبسه حرام وغُذِي بالحرام، فأنى يستجاب لذلك؟)
(رواه مسلم)

(....... Sannan Ya Ambaci Wani Mutum Mai Yawan Tafiya  Ya ɗaga Hannunsa Sama yana Cewa Ya Ubangiji Ya Ubangiji. Alhalin Abincinsa Na Haramun Ne Abin Shansa Haramun Ne, Tufafinsa daga Haramun Ne, An Ciyar Dashi da Haram! To Taya Za'a Amsa Masa?).
{Muslim Ya Ruwaitoshi}

Wannan Hadisin Sai Yake Tabbatar Mana da Cewa Lallai Ta'amuli da Haramun Yana Daga Cikin Dalilan Dakesa Ubangiji Ya Ƙi Amsar Addu'an Bawa.

YA ALLAH KA SANYA MANA ƘYAMAR HARAMUN A RAYUWAR MU, KA BIYA MANA BUƘATUN MU SANNAN KAYI MANA MAGANIN ABINDA YAFI ƘARFIN MU


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Amfanin Daga Hannun Yayin Addu'a "

Post a Comment