Muhimmancin Yin Sallar Walha

ALBISHIRINKA MAI YIN SALLAR WALLAHA

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

Sallar Wallaha sallace ta nafila da ake yinta idan rana ta fito ta dan daga kadan,Hukuncinta Sunnah ce mai karfi daga cikin Sunnonin Manzon Allah SAW,kuma ana daina sallar Wallaha gab da zawalin rana daga tsakiya kuma anfi son yinta idan rana tayi zafi sosai lokacin da mutane suka shagaltu da aiyukan duniya,mafi karancinta raka'a biyu ce mafi yawancinta baya da iyaka, amma Manzon Allah SAW yayi raka'a takwas amma mafi kyakkyawan abin koyi shine Manzon Allah SAW.

1-ALBISHIR NA FARKO
Babu mai kiyaye sallar Wallahi sai bayin Allah masu komawa zuwa ga Allah acikin al'amuransu

Daga Abi Hurairataﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ, daga Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana cewa: (Babu mai kiyaye yin sallar Wallaha sai masu komawa zuwa ga Allah, domin salla ce ta bayin Allah masu komawa zuwa ga Allah)
@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ

2-ALBISHIR NA BIYU
Yin sallar Wallaha raka'a biyu a Masallaci yana daidai da ladar aikin Umara cikakkiya.

Yin sallar wallaha a Masallacin ba tare da dauwama akan hakan ba, yinta lokacin zuwa wani lokacin sunnah ne kuma babu laifi,amma dauwama kullum yinta a Masallaci yau da gobe ya sabawa sunnah, Allah ne Mafi sani.

Daga Abi Umamata ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ daga Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yace:
(Wanda ya fita daga gidansa, yana da alwala zuwa ga sallar farillah, ladar kamar ladar aikin hajji ne mai alfarma,amma wanda ya fita don sallar nafilar wallaha a Masallaci ba abinda ya fitar da shi sai dan ya sallaci sallar wallaha, ladarsa kamar ladar aikin Umara ne,.......)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻮﺩﺍﻭﺩ ﻓﻲ ﺳﻨﻨﻪ ‏( 558 ‏) ، ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻻﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ ‏( 320 ‏)

3-ALBISHIR NA UKU
Sallar wallaha hanya ce ta samun kariya ta Allah ta musamman tun daga farkon yini har zuwa karshen yini.

Daga Abid Dardaa'i da Abi Zarri  ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ daga Manzon Allah ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ yace:
(Allah mai girma da Buwaya yace:YA KAI DAN ADAM,KAYI MIN RAKA'A GUDA HUDU A FARKON YINI ZAN ISAR MAKA ZUWA KARSHEN YININKA)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 437 ‏) ، ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ

Allah zai kareka daga sharri da abin cutarwa zuwa karshen yini kuma ya baka garkuwa daga zunubai da sabon Allah.

4-ALBISHIR NA HUDU
Yin sallar Wallaha yana sauke Ladar sadakar da aka dorawa kowace gaba a kowane yini da rana take bullowa, kuma sallar Wallaha raka'a biyu kadai tana daidai yin sadaka sau 360.

Daga abi Zarri ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ daga Annbi ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ yace:
(Kowace gaba ta dan Adam tana wayuwar gari a tare da ita akwai aikin sadaka da aka dora mata,Kowace Subhanallah sadakace, kowace Alhamdulillahi sadaka ce, kowace Laa'ilaha illallah sadakace, kowace Allahu akbar sadakace, umarni da kyakkyawan aiki sadakane hani akan mummunan aiki sadakane, kuma yana isar maka dukkan wadan nan sadakokin yin sallar wallaha raka'a guda biyu)
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 1181 ‏) .

5-ALBUSHIR NA BIYAR
Samun gidan aljanna guda daya ko guda biyu ga wanda yayi sallar wallaha raka'a Takwas.

Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana cewa: (Wanda yayi sallar Wallaha raka'a hudu kuma yayi wasu hudun kafin wannan na farko, yana da gida a aljanna).

A wata riwayar yana cewa: (Yana da gidaje guda biyu a aljanna)
@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ.

6-ALBISHIR NA SHIDA
Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya kasance yana yin sallar wallahi yau da gobe yana kiyaye yinta saboda ladarta da falalar ta.

Daga A'isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tana cewa:
"Manzon Allah ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ya kasance yana yin sallar Wallaha raka'a hudu kuma yana kara abinda Allah ya so".
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 1176 ‏)

7-ALBISHIR NA BAKWAI
Sallar wallaha wasiyyace daga cikin Manyan wasiyyoyin Manzon Allah SAW ga Manyan Sahabbansa masu girma

Daga Abi Hurairata ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻪُ yace:
"Zababban Masoyina Annabi SAW yayi min wasiya akan kada in sake in bar aikata abubuwa guda ukku:

a-Sallar wallaha
b-Sallar Wutiri kafin ayi barci
c-Azumi uku a kowane wata)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 1178 ‏) ، ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 721 ‏)

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Muhimmancin Yin Sallar Walha"

Post a Comment